Aosite, daga baya 1993
James Lawrenceson, shugaban cibiyar huldar dangantakar Australiya da Sin na jami'ar fasaha ta Sydney, ya ce galibin kasashen Asiya da tekun Pasifik na son daukar hanyar samun bunkasuwa sosai. Domin tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta kamar sabuwar annobar kambi, akwai bukatar mambobin kungiyar APEC su hada kai domin tunkararsu.
Manazarta da dama sun ce, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasifik. Masanin kasar Malaysia Azmi Hassan ya yi imanin cewa, kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka na gina kasa mai bude kofa da bude kofa ga kasashen waje, da sa kaimi ga samar da 'yancin yin ciniki da zuba jari tare da aiwatar da ayyuka masu inganci, kana tana sa ran kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga kafa yankin ciniki cikin 'yanci na Asiya da tekun Pasifik. Har ila yau, Cai Weicai ya yi imanin cewa, kasar Sin ta kasance jagora bisa misali, da daukar matakai masu amfani, wajen inganta cinikayya cikin 'yanci a duniya, wanda zai taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya.
Shugaban cibiyar binciken manyan tsare-tsare ta Asiya ta sabuwar kasar Malaysia Weng Shijie ya bayyana cewa, shawarar da kasar Sin ta gabatar na gina al'ummar Asiya da tekun Pasifik mai makoma guda daya ta dace da halin da ake ciki a yankin Asiya da tekun Pasifik, kuma shi ne wuri mafi dacewa wajen sa kaimi ga hadin gwiwa da dunkulewar yankin. .